Bangaren kasa da kasa, tsohon shugaban kungiyar nan ta masu kishin islama da suka lashe zaben kasar Tunisia wato Al-nahda ya bayyana cewa dole ne kundin tsarin mulkin kasar ya kasance kan koyarwar kur’ani da kuma sunnar ma’aiki da koyarwar addini muslunci.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo na middle-east-online cewa, tsohon shugaban kungiyar nan ta masu kishin islama da suka lashe zaben kasar Tunisia wato Al-nahda ya bayyana cewa dole ne kundin tsarin mulkin kasar ya kasance kan koyarwar kur’ani da kuma sunnar ma’aiki da koyarwar addini muslunci daidai da fahimta da dukaknin bangarori suka amince da ita.
A wani labarin kuma jiragen yakin ruwa guda biyu mallakin Jamhuriyar Musulunci ta Iran sun karasa zuwa tashan jiragen ruwa Tatus da ke kasar Syrai a yau Asabar. A yau din ne jiragen biyu suka tsallaka mashigar ruwa ta Swiz a kasar Masar suka fada cikin tekun Medeteranina, wannan dai shi ne karo na biyu a wannan shekarar wanda jiragen ruwan yaki na kasar Iran suke tsallakawa zuwa tekun Medeteranian.
Rear Admiral Habibullah Sayyari ya fadawa gidan television na PressTv wanda ke watsa shirye shiryensa da harshen turanci a nan Tehran cewa, manufar zuwan wadan nan jiragen ruwa shi ne bawa sojojin kasar Syria horo bisa yerjejeniyar da ke tsakanin kasashen biyu.
Sayyari ya kara da cewa shigar Jiragen ruwan yakin kasar Iran yankin Medeterianian har'ila yau yana nuna irin karfin sojen da kasar take da shi da kuma isar da sakon zaman lafiya ga kasashen yankin.
956014