IQNA

Akasarin Mutanen Kasar Syria Suna Goyon Bayan Shugaba Bashar Asad

22:30 - February 20, 2012
Lambar Labari: 2277793
Bangaren kasa da kasa, gwamnatin kasar Syria na shirin gudanar da kuria’r jin ra’ayin jama’a dangane da sabon kundin tsarin mulkin kasar wanda zai bayar da dama ga mutanen kasar su zabi wanda suke so, sabanin abin da kafofin yada labarai na kasashen turai da na larabawa suke watsawa kan rikicin kasar ta Syria.
Shugaban kasar Syria Bashar Asad ya sanar da ranar 26 ga wannan wata na Fabrairu da muke ciki a matsayin ranar gudanar da kuri'ar raba gardama kan sabon kundin tsarin mulkin kasar, wanda idan akasarin al'ummar kasar suka amince da shi, to zai maye gurbin kundin tsarin mulkin kasar da ake amfani da shi, wanda aka rubuta acikin shekara ta 1973.
A cikin wannan makon ne kwamitin tsara sabon kundin tsarin mulkin ya kammala aikinsa, kuma ya mika shi ga shugaba Bashar Asad domin yin dubi a cikinsa, daga nan kuma za a mika shi ga majalisar dokokin kasar, bayan nan za a ji ra'ayin jamar kasar a kansa.
Sabon kundin tsarin mulkin kasar ta Syria dai yana dauke ne da canje-canje da dama ta fuskacin harkokin siyasa da mulki a kasar, wanda ake ganin cewa idan har aka amince da shi a matsayin kundin tsarin mulki a kasar, to zai zama abin buga misali da shi ta fuskar demokradiyya a cikin kasashen kasashen larabawa.
Daga cikin muhimman abubuwan da sabon kundin tsarin mulkin na kasar Syria ya kunsa, har da dokar kayyade wa'adin shugabancin kasar a cikin shekaru bakwai, kuma za a iya zabar shugaba a wa'ai na biyu, amma daga nan ba zai sake yin shugabanci a kasar ba.
Sa'anan kuma al'umma ne za su zabi shugaban kasa da kansu, maimakon zaben shi a majlaisar dokoki, kamar yadda sabon kundin tsarin mulkin ya bayar da damar kafa jam'iyun siyasa ba tare da wani haddi ba, kuma babu wani fifiko ga wata jam'iyya a kan wata. Haka nan kuma shugaban kasa dole addininsa ya zama muslunci, amma bisa sharadin zai girmama sauran addinai da ke kasar naki daya ba tare da nuna banbanci a tsakanin mabiyansu ba.
A wani bangare na sabon kundin tsarin tsarin mulkin kasar, ya bayar da 'yancin bude kafofin sadarwa masu cin gishin kansu, da kuma damar gudanar da taruka na siyasa da 'yancin bayyana ra'ayi, haka nan kuma bangaren shari'ar kasar zai kasance mai zaman kansa, tare da shiga kafar wando daya da duk wanda ya aikata laifi komai matsayinsa, da kuma yakar cin hanci da rashawa a dukaknin bangarorin gwamnati, da ma tsakanin jamaa'a, kamar yadda hukumar zabe za ta kasance mai cikakken iko da cin gishin kanta, ba tare da karbar umurni daga wani bangare da ke cikin siyasar kasar ba, da ma dai sauran batutuwa da dama da sabon kundin tsarin mulkin ya kunsa.
Masu bin digging lamurran da ke kai da komowa sun amannar cewa, idan al'ummar kasar Syria suka amince da wannan sabon kundin tsarin mulki, kuma aka samu damar aiwatar da dukaknin abin da ya kunsa, to hakan zai mayar da kasar abin koyi ta fuskacin demokradiyya ga sauran kasashen larabawan yankin gabas ta tsakiya, wadanda akasarinsu ba su taba sanin wani abu demokradiyya a cikin kasashensu ba, inda sarki ne wuka da nama a cikin dukaknin harkokin mulki da siyasa a kasa.
956140

captcha