Bangaren fikira, a koda yaushe dan adam yana da bukatar yin aiki na gari saboda Allah madaukakin sarki da niyar kusanci da shi ta hanyar aikata wannan aiki, domin kuwa ta hakan ne zai samu karfafa ruhinsa da ciyar da shi da abincin da yake bukata na tsoron Allah da yin da’a gare shi.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto cewa, Hoj. Eslam Dr. Muhammad Taqi Fali malamin jami’a da kuma cibiyar ilimi da bincike kan ilmomin addinin muslunci ta Hauza ya bayyana cewa, dan adam yana da bukatar yin aiki na gari saboda Allah madaukakin sarki da niyar kusanci da shi ta hanyar aikata wannan aiki, domin kuwa ta hakan ne zai samu karfafa ruhinsa da ciyar da shi da abincin da yake bukata na tsoron Allah da yin da’a gare shi gwargwadon iko.
Dangane da lokutan ibada masu muhimamnci a muslunci, daren lailatul Qadr na daga ciki, an samu sabanin ruwayoyi da dama da suka zo daga manzon rahama da kuma iyalan gidan sa tsarkaka wajen ayyana daren lailatul kadr, bayan cimma daidaito a kan cewa yana cikin watan ramadan ne. A cikin wasu ruwayoyi ana ganin boyewa da asirtawa da aka yi a kan muhimmancin daren an yi hakan ne saboda wata manufa, domin bayar da dama bawa na gari ya kara kaimi wajen aikata ayyukan na kwarai, da adduo'i da komawa ga Allah da kaskantar da kai gare shi madaukakin sarki, da ciyarwa da yawaita sallah da dai sauran ayyukan ibada. Kamar yadda aka tambayi Imam ma'asumi daga cikin iyalan gidan manzo a cikin wasu ruwayoyi game da Lailatul kadr cewar wanne dare ne? shin daren ashirin da daya ne? ko kuma talatin da uku? Sai dai bai ayyana ko daya daga ciki ba, sai ya ce: "mane ne yafi sauki cikin abin da kake neman a wadannan darare biyu" Sai ya ce : "ka aikata dukkan abin da ke gareka na alkhairi a cikin wadannan darare biyu."
Abin da yake sananne daga cikin dararen da aka fi tsammanin kasancewar daren Lailatul kadr a cikinsa shi ne daren goma sha tara ga watan Ramadana, da kuma daren ashirin da daya da kuma ashirin da uku, amma dai nakarshe shi ne yafi shahara kamar yadda ya zo a cikin wasu ruwayoyi masu yawa, kuma ita ce aka fi sani da daren jahni.
Wani mutum daga cikin muslmai da suke zaune a wajen birnin madina, hakika ya tambayi Manzom Allah da ya ayyana masa daren Lailatul kadr domin ya kebance kansa a cikinsa da ibada, sai Manzo ya ayyana masa daren ashirin da uku. to kila abin da yake nuni zuwa ga hakikanin wannan lamari shi ne cikakken bayani da ya zo a cikin ayyukan daren ashirin da uku.
Hakika wasu nassoshi sun yi magana game da haka kamar addu'a misali: "ya ubangiji nayi yammaci ina bawa gareka." Wanan shi ne abin da Imam Zainul Abidin yake yawaita addua'a da shi a cikin wannanan dare bisa abin da Kaf 'ami ya Rawaito, haka ma addu'ar Jaushunal Kabir da Sagir, domin wannan addu'ar tana kunshe da wasu abubuwa na musamman a layukan karshe guda uku, kari a kan abin dake tattare da ita na raya shi da ibada a cikin wannan dare.
Hakika daren goma sha tara ga wata an kebance shi da yawan yin Istigafari sau dari a cikinsa, da kuma tsine wa wanda ya kashe Amirul Mu’aminin Ali Sau dari, domin a wannan daren ne aka Sari Amirul Mu'aminina Ali a cikinsa da hannun Abdurahman Ibn Muljam khariji (tsinuwar ubangiji ta tabbata gare shi)
Kamar yadda ake karfafa yin addu'oin nan guda biyu na musamman a cikin dararen watan ramadan kamar:" ya Ubangiji ka sanya a cikin al’amuran da ka hukumta kuma ka kaddara" da kuma addu'ar ya wannan wanda ya kasance."
Amma daren ashirin da daya na daga cikin dararen da aka fi sani da dararen lailatul kadr shi ne wanda aka fi tsamamanin amun daren a cikinsa fiye da sauran wadanda suka gabata. daga nan sai ya fara ayyuka da addu'oin kwanaki goma na karshe na watan ramadan wanda aka kebance ta da su.
Yawaita rayasu da ibada, domin manzon Allah ya kasance yana nade shimfidarsa sannan ya zage damtsen sa wajen yin ibada a cikin kwanaki goma karshe na watan ramadan, ya kasance yana lizimtar masallaci ya dukufa a cikinsa.
Hakika an yi bayanai game da muhimmacin dake tattare da raya shi da yawan yin sallah da Addu'a da kuma salati ga manzo da iyalan gidansa tsarkaka, da kuma tsine wa wadanda suka zalunci manzo da iyalan gidansa tsarkaka, tun da a cikinsa ne Amirul muminin Ali ya yi shahada kuma ana so a yawaita karanta ziyarar Imam Hussain a ranar.
Amma daren ashirin da uku shi ne mafificin dare kamar yadda muka ambata. Domin kuwa ya zo da wasu ayyuka na musamman a cikinsu, su ne karatun alkur'ani, musamamn ma wasu surori kebantattu, misali kamar Surar Ankabut, da Rum da Dukhan, da kuma surar Kadr sau dubu, haka ma ya karfafa game da karanta ziyarar Imam Hussaini.
Hakazalika karanta ziyarar Imamul Hujja kamar haka: ya Ubanjigi ka sanya ga masoyinka alhujjatu binul Hassan salatinka su tababbata gare shi da iyayensa baki daya, a cikin wannan lokaci da ma kowanne lokaci masoya, da masu kiyayewa, da kuma jagoranci da mataimaki, da kuma hujjah har sai ka tababbatar da shi a cikin kasa, cikin nastuwa kuma ka rayar da shi a cikinta lokaci mai tsawo. An so a rinka maimaita wanann addu'ar a lokuta daban-daban kamar yadda yake mustahabi ne a hada ta da wasu Addu'oi da aka kawo a cikin littafan Addu'a.
Daga karshe yana da kyau a yi la'akari da dararen lailatul kadr, domin ranar lailatul tana da matsayi na musamman da ya yi kama da darajar daren lailatul kadr, kamar yadda ya zo a cikin wasu ziyarori da aka yarda da su kuma ya yi kama da abin da daren lailatul kadr yake da shi da ranar juma'a inda yake samu muhinmanci daga daren juma'ar kanta.
917198