Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya naklato daga shafin sadarwa na yanra gizo cewa, mabiya addinin muslunci a kasar Belgium sun yi kakkausar suka dangane da keta alfarmar wani masallaci da wasu masu tsatsauran ra’ayin kymar muslmi a kasar suka yi da nufin yin tsokana ga musulmi ta yadda hakan zai zama wani masomin tashin hankali a kasar.
A wani labarin kuma majalisar malaman addinin muslunci a kasar Sudan ta fitar da wani bayani da a cikinsa take cewa al’ummar kasar ba su bukatar wani abu ya zama tsarinsu na rayuwa tare da yin kira da a kara baiwa wannan bangare muhimmanci a matukar a cikin dukaknin harkokin mulki da siyasa a fadin kasar.
Kakakin rundunar sojin kasar Sudan ya bayyana cewar sojojin gwamnatin Sudan ba su kaddamar da wani hari kan 'yan tawayen kasar ba a cikin 'yan kwanakin nan, ballantana kai hare-hare kan yankunan jihohin kudancin Kordofan da Blue Nile, don haka da'awar kasar Amurka na cewa sojojin gwamnatin Sudan sun kai hare-hare kan yankunan jihohin biyu karya ce tsagwaronta.
A ranar juma'ar da ta gabata ce dai jakadiyar kasar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Suzan Rice ta yi da'awar cewa; sojojin gwamnatin Sudan sun kai hare-hare kan yankunan jihohin kudancin Kordofan da Blue Nile, tare da yin Allah wadai da hare-haren.
957704