IQNA

Imam Musa Sadre Abin Koyi Ne A Fagen Tattaunawa Ta Addini

Bangaren kasa da kasa; Imam Musa Sadre yana daga cikin wadanda suka bukaci al'ummar klasar Labanon zuwa ga sulhu da fahimtar junansu ta hanyar tattaunawa da zama kan teburin tattaunawa da masanyar ra'ayi a kokarin magance duk wani sabani day a hada da na addinai ko na kabila don haka wannan wani abin koyi ne ga duk wani mai son sulhu da zaman lafiya da fahimtar juna a fadin wannan duniya.



Kamfanin dillancin labarai na ikna ne da ke kula da harkokin kur'ani mai tsarki a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: Imam Musa Sadre yana daga cikin wadanda suka bukaci al'ummar klasar Labanon zuwa ga sulhu da fahimtar junansu ta hanyar tattaunawa da zama kan teburin tattaunawa da masanyar ra'ayi a kokarin magance duk wani sabani day a hada da na addinai ko na kabila don haka wannan wani abin koyi ne ga duk wani mai son sulhu da zaman lafiya da fahimtar juna a fadin wannan duniya. A yau wannan duniya ta mu tana bukatar samar da wata hanya ta tattaunawa da fahimtar juna musamman ana iya amfani da kafafen watsa labarai day a hada talbijin da radiyo da masana da kwararru da malaman addini da shugabannin addini da na kabilu da kuma duk wannan lamarin ya shafa domin fadakar da al'ummomi muhimmancin samar da zaman lafiya da zaman lafiya da fahimtar juna da kuma irin alherin da ke tattare da hakan . Har ila yau Imam Musa Sadre wani gimshiki ne da abin koyi a wannan fanni musamman idan aka yi la'akari da rawar day a taka a kasar Labanon.
957842