Bangaren zamantakewa; hukumar da ke kula da harkokin addini ta bukaci hukumta sojojin Amerika da ke kasar Afganistan da suka ci mutunci da fuskar kur'ani mai tsarki inda wasu daga cikin sojojin mamaye na Amerika a kasar Afganistan suka kona kur'aniai kuma neman gafara da gwamnatin amerika ta yi ba zai hana a hukmta wadanda suka aikata wannan danyan aiki kan addinin musulunci da kuma wannan wani salo ne na takalar fada.
Kamfanin dillancin labarai na ikna ne da ke kula da harkokin kur'ani mai tsarki a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: hukumar da ke kula da harkokin addini ta bukaci hukumta sojojin Amerika da ke kasar Afganistan da suka ci mutunci da fuskar kur'ani mai tsarki inda wasu daga cikin sojojin mamaye na Amerika a kasar Afganistan suka kona kur'aniai kuma neman gafara da gwamnatin amerika ta yi ba zai hana a hukmta wadanda suka aikata wannan danyan aiki kan addinin musulunci da kuma wannan wani salo ne na takalar fada. Kungiyar Hizbullahi mai gwagwarmaya a kasar Labanon ta yi Allah wadai da tofin Allah tsine kan yadda wasu sojojin mamaye na Amerika a kasar Afganistan suka ci mutuncin Alkur'ani mai tsarki.Shima Kamfanin dillancin labarai na Jamus ne ya watsa rahoton cewa; a jiya ne kungiyar Hizbullahi a kasar Labanon ta fitar da wata sanarwa mai muhimmanci da a cikinta ta yi Allah wadai da yadda sojojin mamaye na Amerika a kasar Afganistan suka kaita hurumi da cin mutuncin kur'ani mai girama da cewa wannan bakin aiki na sojojin Amerika cin fuska da mutunci ne ga musulmi sama da biliyan daya a duniya .
A daren litinin wayewar jiya ne wasu sojojin Amerika a kasar Afganistan suka kona wasu kur'anai lamarain da ya tilastawa al'ummar biranai da daman a Afganistan da ya hada Kabul fadar mulkin kasar suka gudanar da zanga zanga a jiya domin yin Allah wadai da wannan aiki na ganganci da takalar fada da sojojin Amerika suka yi a Afganistan.
958612