Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Almanar cewa, bababn sakataren kungiyar gwagwarmaya ta Hizbullah sayyid Hassan Nasrullah ya bayyana cewa kone alkur'ani mai tsarki da ake yi a cikin wasu kasashen yammacin turai da hakan ya kai ga har suna zuwa suna yin hakan a cikin kasashen musulmi tunani na yahudawan haramtacciyar kasar Isra'ila day a ginu kan tsananin gab ada addinin muslunci.
Babban sakataren kungiyar Hizbullahi ta kasar Labanon ya yi gargadi kan shirin da makiya ke yi na kunna wutan rikici a yankin gabas ta tsakiya.
A jawabin da ya gabatar kan makon tuna jagororin gwagwarmaya a yau juma'a; Sayyid Hasan Nasrullahi babban sakataren kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullahi da ke kasar Labanon ya jaddada aniyar kungiyarsu ta ci gaba da kare kasar Labanon daga duk wata barazanar makiya, tare da yin tuni kan irin gagarumar rawar da gwagwarmaya ta taka wajen rusa mafi hatsarin shirin Amurka da na haramtacciyar kasar Isra'ila kan kasar Labanon da yankin gabas ta tsakiya baki daya, musamman shirin Amurka na samar da sabon yankin gabas ta tsakiya, inda za a raba kasashen yankin a kan tubali na kabilanci, addini da mazhaba.
Sayyid Nasrullahi ya kuma fayyace irin makirce-makircen da haramtacciyar kasar Isra'ila da uwargijiyarta Amurka da 'yan koransu na kasashen Larabawa ke kullawa na kunna wutan rikici da fitina a dukkanin yankin gabas ta tsakiya, don haka ya bukaci fadakar al'umma domin tunkarar wannan makirci.
959405