IQNA

Sheikh Hassan Saffar Ya Yi Allawadai Da Cutar Da Musulmi Shi'a Da Ake Yi A Saudiyya

16:00 - February 25, 2012
Lambar Labari: 2280216
Bangaren kasa da kasa, daya daga cikin fitattun malaman mabiya tafarkin iyalan gidan manzon allah a kasar saudiyya ya yi kakkausar suka da yin Allawadai da matakan da mahukuntan kasar suke dauka na murkushe da haramta musu hakkokinsu.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na rasid cewa, Sheikh Hassan Saffar daya daga cikin fitattun malaman mabiya tafarkin iyalan gidan manzon allah a kasar saudiyya ya yi kakkausar suka da yin Allawadai da matakan da mahukuntan kasar suke dauka na murkushe da haramta musu hakkokinsu, maimakon haka ma ana ci gaba da yi musu kisan kiyashia lokacin da suka nemi wadannan hakkokin.
Bayanin ya ci gaba da cewa malamin ya jadda muhimmancin yin adalci a tsakanin mutanen kasar baki daya ba tare da nuna bangaranci ko wariya ga wasu ba, ko da kuwa su ne marassa rinjaye, domin kuwa a cewarsa kasar ta dukaknin mutanen kasar ce baki daya, kamar yadda dukaknin hakkokinsu wajibi ne a bas u.
Malamin wanda daya ne daga cikin fitattun malaman mabiya tafarkin iyalan gidan manzon allah a kasar saudiyya ba ya ga kakkausar suka da yin Allawadai da matakan da mahukuntan kasar suke dauka na murkushe 'yan shi'a, ya ce hakan ne zai sanya mutane su yi abin da mahukuntan kasar suke tsoro.
959266

captcha