IQNA

Kungiyar Da ke Kula Da Ahlul Baiti (AS) Ta Yi Allah Wadai da Cin Mutuncin Kur'ani

Bangaren kasa da kasa; kungiyar da ke kula da lamarin day a shafi mabiya ahlul baiti (AS) a duniyata fitar da wani bayani da a cikinsa take suka da yin Allah wadai da yadda wasu sojojin mamaye na Amerika a kasar Afganistan suka ci mutuncin Kur'ani mai girma a birnin Kabul.





Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai tsarki a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: kungiyar da ke kula da lamarin day a shafi mabiya ahlul baiti (AS) a duniyata fitar da wani bayani da a cikinsa take suka da yin Allah wadai da yadda wasu sojojin mamaye na Amerika a kasar Afganistan suka ci mutuncin Kur'ani mai girma a birnin Kabul. Kungiyar ta kara bayani da cewa makiya addinin musulunci yadda musulmi ke kara samin hadin kai da fadaka da suke ci gaba da samu ne ke bakanta masu da rai don haka suke daukan matakai na takalar fada da kuma cin mutunci abubuwa na addini da masu kima na addinin musulmunci. To ya kamata makiya addinin musulunci da musulmi su kwan da sanin cewa babu wani abu da za su iya kuma duk wani mataki da suke dauka irin wannan babu abin da zai kara sai karfin guiwar tunkararsu da kawo karshen makircinsu a kasashen musulmi .Kuma musulmi a fadin duniya na yin Allah wadai da irin wannan mataki na kona Kur'ani mai girma da makiya ke yi a kasashen musulmi da suka mamaye.
958722