IQNA

Limaman Masallatan Juma’a A Gabacin Saudiyya Sun Goyi Bayan Saffar

18:12 - February 26, 2012
Lambar Labari: 2281196
Bangaren kasa da kasa, da dama da gac ikin limaman masallatan juma’a a yankin gabacin kasar Saudiyya sun nuna cikakkaen goyon bayansu ga malamin da yake fuskantar barazana da mahukuntan kasar bayan da yi suka kan kisan kiyashin da ake yi wa al’ummar yankin katif masu neman sauyi.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Rasid cewa, limaman masallatan juma’a a yankin gabacin kasar Saudiyya sun nuna cikakkaen goyon bayansu ga malamin da yake fuskantar barazana da mahukuntan kasar bayan da yi suka kan kisan kiyashin da ake yi wa al’ummar yankin katif masu neman sauyi a cikin harkokin siyasa da mulki a kasar.
Kungiyar kare hakkin bil'adama ta kasa da kasa "Amnesty International "ta bukaci a gudanar da bincike akan kisan da jami'an tsaro su ka yi wa wani mai zanga-zanga a gabacin saudiyya, a wani bayani da kungiyar ta kare hakkin bil'adama ta fitar ta bukaci a yi bincike mai zaman kanshi akan kisan da aka yi wa Isam Muhammad Abu Abdullah a lokacin da ya ke cikin zanga-zanga a garin Awamiyyah da ke gabacin Saudiyya.
Bayanin kungiyar ya ci gaba da cewa: "Zanga-zangar ranar alhamis din da ta gabata an yi ta ne domin kira da a saki fursunonin siyasa da ake tsare da su da kuma kawo karshen wariyar da ake yi wa 'yan shi'a a yankin, a cikin watannin bayan nan dai jami'an tsaron Saudiyya sun rika bude wuta akan masu zanga-zangar lumana da su ke son a samar sa sauye-sauye na siyasa a cikin kasar.
959976




captcha