Bangaren kasa da kasa: ma'aikatar sadarwa ta kasar Marokko ta bayyana cewa; ta shirya wani shiri na yaki da masu tsananin ra'ayin addini tare da hada baki da marubuta na yammacin Turai.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai tsarki a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: ma'aikatar sadarwa ta kasar Marokko ta bayyana cewa; ta shirya wani shiri na yaki da masu tsananin ra'ayin addini tare da hada baki da marubuta na yammacin Turai. An nakalto daga majiyar labarai ta Afriquehebdo cewa: Mustapha Alkhalafi kakakin gwamnatin marokko a wani taron manema labarai ya bayyana cewa; ma'aikatar sadarwa da hulda da manema labarai tana nan ta shirya za ta taimakawa hukumomin ilimi da na al'adu karkashin kungiyar hadin kan kasashen musulmi Asesko domin shirya wani shiri na yakar masu tsananin addinin musulunci da ke shafawa musulmi da addinin musulunci kashin kaji da fata masu suna . Ya kara da cewa sun guduri aniyar yaki das a kafar wando guda da masu batawa addinin musulunci suna da kuma za su fara wannan gwagwarmaya ne ta hanyar kafafen watsa labarai.
959654