IQNA

'Yan Salafiyya Ba Su Da Wuri A Cikin harkokin Mulki Da Siyasar Tunisia

20:29 - February 27, 2012
Lambar Labari: 2281967
Bangaren kasa da kasa, 'yan salafiyya ba su da wuri a cikin gwamnatin rikon kwaryar da aka kafa a kasar Tunisia saboda matsayarsu a kan lamurra da dama da suka danganci gwamnatin tsohon shugaban mulkin kama karya na kasar da suke goyon bayansa.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo na business news cewa, minister a kasar Tunisia Muhammad Abbu ya bayyana cewa, 'yan salafiyya ba su da wuri a cikin gwamnatin rikon kwaryar da aka kafa a kasar Tunisia saboda matsayarsu a kan lamurra da dama da suka danganci gwamnatin tsohon shugaban mulkin kama karya na kasar da suke goyon bayansa, saboda kykakkyawar dangatakar da ke tsakaninsa da kasar da ke daure musu gindi.

A wani labarin kuma Akalla mayakan kungiyar Alshabab 4 ne aka tabbatar da sun rasa rayukansu a wata musayar wuta da suka yi da dakarun gwamnatin rikon kwaryar kasar, mai aiko ma gidan talabijin Al-alam rahotanni daga kasar Somalia ya habarta cewa, wannan taho mu gama ta zo bayan kaddamar da wani farmaki da mayakan Alshabab suka yi a kan wani sansanin dakarun gwamnatin rikon kwaryar Somalia da ke yankin Bakool a yammacin kasar, inda dakarun na gwamnati suka mayar da martani da manyan bindigogi masu aman wuta, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar 4 daga cikin mayakan alshabab.
960317

captcha