Kamfannin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani ami girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: al'ummar kasar Suriya a ranar lahadi bakwai ga watan Isfand na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya sun kasance a gaban akwatunan zabe domin zabar sabon kundin tsarin mulki a kasar da kuma zai canja rayuwar mutane sama da miliyan ashirin. A dabra da haka Shugaban kasar Siriya Bashar al-Asad ya sanya hannu kan sabon kundin tsarin mulkin kasar da mafi yawa daga cikin al'ummar kasar suka amince da shi a kuri'ar jin ra'ayin al'umma da aka gudanar kansa a ranar lahadin da ta gabata.
Rahotannin da suke fitowa daga kasar Siriyan suna nuni da cewa a daren jiya litinin ne shugaba Asad din ya sanya hannu kan sabon kundin tsarin mulkin wanda ya ke nufin a hukumance an amince da shi a matsayin kundin tsarin da ke mulki a kasar.
Manyan kasashen duniya irin su Rasha da China sun amince da wannan shiri na sauyi da shugaba Asad din ya shigo da shi da kuma amincewa da sabon kundin tsarin mulkin da al'umma suka yi, alhali kuwa sauran kasashen yammaci da wasu na larabawa suke ci gaba da makirce-makircen da suke yi wa kasar da nufin kifar da gwamnatin shugaba Asad din don cimma wata manufa ta su.
A bisa sanarwar da ma'aikatar cikin gidan kasar ta fitar, an bayyana cewar kimanin kashi 57 cikin dari na mutanen kasar ne suka kada kuri'unsu a wannan zabe duk kuwa da kiraye-kirayen da 'yan adawa suka yi na a kaurace masa, sannan kuma kimanin kashi 89.4 cikin dari ne suka amince da sabon kundin tsarin mulkin.
961389