Bangaren siyasa da zamantakewa: rahmi Anurshan ya bayyana cewa kungiyoyi masu tsautsauran ra'ayin riko na addinin musulunci ta hanayr kafirta yan uwansu musulmi masu bin sauran mazhabobi na musulunci ko sun sani ko bas u sani ba a wajan musulunci na bata sunan musulmi da addinin musulunci da kuma aiwatar da aiki dab a shi da wani banbanci da na makiya.
Kamfannin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani ami girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: rahmi Anurshan ya bayyana cewa kungiyoyi masu tsautsauran ra'ayin riko na addinin musulunci ta hanayr kafirta yan uwansu musulmi masu bin sauran mazhabobi na musulunci ko sun sani ko bas u sani ba a wajan musulunci na bata sunan musulmi da addinin musulunci da kuma aiwatar da aiki dab a shi da wani banbanci da na makiya. A wani taron wuni daya da aka gudanar a Istambul na kasar Turkiya da aka samu halartar masana da kwararru da masu sha'awar kur'ani mai girma da ilmi na addinin musulunci suka halarta a taron da aka bawa taken Kur'ani da ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayansasun bayyana rashin jin dadi dab akin cikin ganin yadda wasu masu nuna tsananin ra'ayin addinin musulunci ke kafirta yan uwansu musulmi a daidai wannan lokaci da makiya addinin musulunci ke yawaita kai hare hare da nuna kama kan duk wani musulmi a duniya ko yanada tsautsauran ra'ayin addini ko ya san hawa ko bai san sabka ba . Mahalartar wannan taron sun bukaci sauran yan uwansu musulmi da hadin kai da kawo karshen kafirta juna da duk wani sabani da ke tsakani kuma kowa ya yi aiki da akida da fahimtar day a amince da ita ba tare da tashin hankali da halarta jinin yan uwa ba.
961253