IQNA

Zaben Raba Gardama A syria Kan Kundin Tsarin Mulki Ya Kunyata Makiya Asad

16:45 - February 28, 2012
Lambar Labari: 2282675
Bangaren kasa da kasa, a daidai lokacin da makiya al’ummar kasar Syria suke ta kai gwabro sukai mari domin ganin sun kawo rashin zaman lafiya da fitina a cikin sai ga sabon kundin tsarin mulki wanda ya kunyata masu gaba da shugaban kasar Bashar asad.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, lokacin da makiya al’ummar kasar Syria suke ta kai gwabro sukai mari domin ganin sun kawo rashin zaman lafiya da fitina a cikin sai ga sabon kundin tsarin mulki wanda ya kunyata masu gaba da shugaban kasar Bashar Asad da suka bayyana kowa ya gansu a zahiri.
An gudanar da kuri'ar raba gardama kan sabon kundin tsarin mulkin kasar Syria a dukkanin jahohin kasar, tare da halartar akasarin wadanda suka cancanci kada kuri'a a kasar, duk kuwa da kiran da wasu 'yan adawa suka yi na a kaurace ma zaben, rahotanni daga kasar ta Syria sun habarta cewa, an rufe runfunan zabe ne a mafi yawan jahohin kasar da kimanin karfe goma na daren jiya Lahadi, bayan da aka kara sa'oi uku kayayyaden lokacin da aka ambata.
Da dama dag acikin wadanda suka kada kuri'arsu sun nuna matukar gamsuwarsu da sabon kundin tsarin mulkin na kasar Syria, wanda ya bayar da dammar kafa jam'iyun siyasa babu iyaka, tare da bayar da cikakken yanci na siyasa da fadar albarkacin baki da kayyade wa'adin mulki zuwa wa'adi daya ko biyu kawai, tare da bayar da ilimi da kula da kiwon lafiyar 'yan kasa kyauta.
Rahotanni daga birnin Homs sun tabbatar da cewa an gudanar da zaben lami lafiya, duk kuwa da musayar wutar da ake yi a unguwar Baba Amru inda a halin yanzu nan ne 'yan bindigar kasar suka kafa tungarsu, dakarun gwamnati na ci gaba da kokarin dawo da doka da oda a cikin unguwar da kewayenta, tare da fatattakar 'yan bindiga.
960519
captcha