Bangaren kasa da kasa, dogaro da hadisan ma’aiki da Imam ali su ne babbar madogara a cikin dukaknin lamarin irfani a cikin addinin addinin muslunci, kuma yin wani abu sabanin koyarwarsu ba lissafa shia ackin irfani na koyarawar addinin muslunci.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Hoj. Eslam Dr. Muhammad Taqi Fali malamin jami’a da kuma cibiyar ilimi da bincike kan ilmomin addinin muslunci ta Hauza ya bayyana cewa, yin dogaro da hadisan ma’aiki da Imam ali su ne babbar madogara a cikin dukaknin lamarin irfani a cikin addinin addinin muslunci, kuma yin wani abu sabanin koyarwarsu ba lissafa shi a cikin irfani na koyarawar addini.
A cikin hadisai da Mahangar ahlul baiti zamu samu cewar lallai wannan tsarki da wasu sashin bangarorinsa suna yaduwa zuwa ga sauran wurare daban daban, misali kamar gidan manzo da iyalan gidansa, da hubbarorinsu masu tsarki da kuma sauran wurare da suke da na tarihi dake da alaka ga Annabawa da salihan bayi daga cikin bayin Allah, inda su wadansu bayin Allah din suka yi salla cikin su, ko yana da alaka da su ko kuma da abin da ya faru da su a wurin.
Wannan ra'ayi ya samo asali ne daga mahangar musulunci game da irin muhimmacin da ya bawa wuraren da suke da alaka da Annabawa da salihan bayi, da kuma irin abubuwa da suka faru da su a lokacin da suke isar da sako, inda aka yi amfanin da ayoyin kurani mai girma, da sauran nasoshi daban daban wajen jawo hankula domin yin la'akari da irin yadda al’kur'ani ya bada muhimmanci ga alamomi da ababen tunawa na tarihi, wanda harkokinsu da mastayinsu ya tabbata a fili ta hanyar nuna godiyar su ga Allah Madaukakin Sarki, kuma aka lizimta adana su da kuma kiyayesu a cikin kundin tarihi.
Akwai yi yuwar a samo asalin wannan fahimtar a cikin wasu abubuwa da suka faru da alkur'ani mai girma ya tabbatar da su, haka ma a cikin sashin wasu alamomi da alkur'ani ya tabbatar da su, kuma ya yi magana a kai, ko kuma wasu ma'anon da aka tabbatar da su a wani bangare na alamomin sakon musulunci, haka ma a cikin tarihin Annabi mai daraja, za mu yi ishara zuwa ga wasu daga cikin wadan nan alamomin:
Na farko: kissar Ashabul kahafi, wanda al-kur'ani ya yi ishara a kai cewar muminan da suka rinjaya a kan alamarinsu a wancan lokacin an riki massalaci a kansu domin girmamawa da jinjinawa ga mastayin wadannan bayin Allah da suka yi tawaye ga bautan gumaka da dagutu. "A lokacin da suke jayayyar al’amarinsu tsakaninsu sai suka ce ku gina wani gini a kansu, Ubanjiginsu ne mafi sani game da su, wadanda suka rinjaya a kan al’amarinsu suka ce lallai mu riki massalaci a kansu.
Na biyu: girmama mukamar ibrahim (as) shi ne wani tubali ko kuma dutse da Annabi Ibrahim yake tsayawa a kai domin gina dakin ka'aba mai daraja. Inda ya zo a cikin alkur’ani game da mustahabbanci ko kuma wajibcin yin sallah a wurin mukamar ibrahim din, bayan ka kammala dawafi kamar dai yadda ya zo a cikin al kur'ani mai girma. "kuma suka riki wurin sallah a makamar Ibrahim." wanann yana daga cikin abin da musulmi suka hadu a kai.
Na uku: na daga abin da ya zo na batun sanya dutsen Annabi Ismal'il a cikin dawafi wato ( hijir isma'il) duk da yake baya daga cikin ginin ka'aba haka nan batun mustahabancin yin sallah a cikinsa, saboda nan ne wajen da aka bizne mahaifiyarsa da ma wasu daga cikin Annabawa, wannan ma yana daga cikin abin da dukkan musulmi suka hadu a kai.
Na Hudu: yana daga abin da ya zo a cikin alkur'ani mai girma na karfafawa game da batun yin sa'ayi tsakanin Safa da Marwa, kuma lallai yana cikin alamomin 'girmamawa na ubangiji kamar yadda ya zo a cikin fadar sa Madaukakin Sarki: "Lallai ne Safa da Marwa suna daga cikin wuraren ibadar Allah, To wanda ya yi hajjin daki ko kuma ya yi Umara to babu laifi a kansa da ya yi dawafi a gare su, su biyu kuma wanda ya kara yin wani aikin alkhairi to lallai ne Allah mai godiya ne kuma masani." (3)
Kamar yadda aka ambata a cikin tarihi irin dangantakar dake tsakanin Sa'ayin da ake yi yanzu da kuma wanda mahaifiyar Annabi Isma'il Hajara ta yi, domin tsamar da danta daga cikin matsananciyar kishin ruwada yake ciki wanda daga karshe ya kai ga ta gano igiyar ruwar rijiyar zamzam.
Hakika Kulaini ya Rawaito daga madogara ingantacciya daga Abi Abdallah Sadiq (as) ya ce : " lallai lokacin da Ibrahim yabar Isma'il a Makka sai kishi ya kama jaririn, kuma ya kasance tsakanin dustin safa da marwa, akwai wata bishiya sai mahaifiyarsa ta fito har sai da ta hau kan dutsin safa sai ta ce: shin ko akwai mataimaki a cikin mutanen kauyen nan? Babu wanda ya amsa mata, sai ta gangara har ta hau kan dutsin marwa kuma ta sake cewa shin akwai mataimaki a cikin wannan kauye? Babu wanda ya ba ta amsa Sannan Sai ta dawo zuwa ga Safa kuma ta sake fadin haka har ta sau bakwai, sai Allah ya maida hakan ya zama sunna ga sauran al’umma.
Na Biyar: yana daga abin da ya zo, girmama Masallacin kudus wato Aksa, domin shi ne alkibilar farko kuma wurin ibadar Annabawa da suka gabace mu. Kuma hanyar Isra'i da Mi'iraji da Manzo ya yi kamar yadda alkur'ani ya yi ishara a kai.
Na Shida: yana daga cikin abin da musulmai suka hadu a kai girmama masallacin (kuba) wanda yake masallacin ne da aka gina shi bisa asasin tsoron Allah tun daga ranar farko kamar yadda kur'ani ya yi ishara a kai, kuma shi ne wurin da manzon Allah ya yi sallah a cikinsa lokacin da ya isa birnin Madina, kuma ya tsaya a cikinsa na dan wani lokaci kafin ya shiga cikin Madina, sai musulmai suka gina masa masallaci a wajen, nan gaba kadan za mu kawo bayani a kai.
Na Bakwai: a cikin abin da Alkur’ani ya tabbatar da shi na daga ma'anar gidajen da Allah ya bada izinin a daukaka kuma a ambaci sunansa a ciki, shi ne gidajen nan da salihan bayi suke zaune a cikinsu, kamar yadda ya ce a fadarsa madaukakin sarki: "A cikin wadansu gidaje wadanda Allah ya yi umarni a daukaka kuma a ambaci sunansa a ciki suna yin tasbihi a gare shi a cikin safiya da marece."
"wadansu mazaje wadanda wani fatauci ba ya shagaltar da su daga ambaton Allah da tsaida sallah da bada zakka suna tsoron wani yini wanda zukata suke bibirgita a cikinsa da gannai."
bisa ga wannan ma'anoni za mu ga cewar saboda yalwataccen i limin da Ahlul baiti suke dashi game na tarihin sakon ubangiji, da kuma zurfin fahimtarsu da abin da ke kunshe da dukkan sakwanni, yasa suka zo da wani aiki da suka yi fice a kai, shi ne raya alamomin uabangiji na girmamawa kuma na tarihi, babu wani banbanci a cikin sakwannin shin ga wadanda suka gabata ne ko kuma a cikin sakon muslunci, tare kuma da yin kira zuwa ga tsarkake wadannan wurare da kuma raya abubuwan tarihin su."
An kebance wa Masallacin harami da kuma na Manzo da ke Madina mai haske da massalacin Aksa wato kudus wani matsayi na daraja, ga gimamawa da kuma ba su wani mastayi na mussaman daga dukkanin musulmi.
910883