Bangaren kasa da kasa, Muhammad Al-duraini babban sakataren majalisar koli ta mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allha akasar Masar kuma shugaban jamiyar Algadir ya bayyana cewa wajibi ne dukaknin bangarorin al’ummar Masar su shiga cikin batun tsara kundin tsarin mulkin kasar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Ala’alam cewa, babban sakataren majalisar koli ta mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allha akasar Masar kuma shugaban jamiyar Algadir Muhammad Al-duraini ya bayyana cewa wajibi ne dukaknin bangarorin al’ummar Masar su shiga cikin batun tsara kundin tsarin mulkin kasar ta yadda hakkin wani bangare daga cikin al’ummar kasar ba zai bata ba.
Muhammad Al-duraini ya kirayi shugaban majalisar sojin kasar da ke mulki da kuma shugaban majalisar dokokin kasar,gami da pitra ministan gwamnatin wucin gadi jamal Ganzuri, da su kirayi dukaknin bangarorin siyasa da ma masu wakiltar wasu al’ummomi a kasar a lokacin kafa kwamitin tsara kundin tsarin muslkin kasar wanda za a nan gaba.
Wakilan majalisu biyu na soji da kuma doki sun fara tattaunawa kan zaben wadanda za su shirya kundin tsarin mulki na kasar Masar, wanda zai maye gurbin tsohon kundin tsarin mulki wanda tsohon shugaban kasar ya shirya.
Wannan kwamiti ne zai dauki nauyin shirya sabon kundin tsarin mulki, wanda kum azai maye gurbin hattakundin tsarin muli kwarkwarya na da sojoji suka shirya. 963678