Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Almanar cewa, Yahya Gaddar shugaban kungiyar hadin gwiwar larabawa da musulmi ya bayyana cewa, manufar matsa lamba kan Syria da sunan ana kare demokradiya ko hankorin tabbatar da ita a kasr daidai da mahangar kasashen turai, manufar hakan ita ce kawar da gqwamnatin Syria da ta tsone ma yan mulkin kama karya ido.
Bayan kwashe kimanin wata guda ana gumurzu tsakanin 'yan tawayen kasar Syria da suke dauke da makamai da kuma jami'an tsaron kasar a unguwar Baba Amru da ke garin Homs, a jiya Alhamis dakarun gwamnatin Syria sun murkushe 'yan bindiga, yayin da wasu sama da 700 suka mika kansu da makaman da ke hannunsu, daga cikinsu kuwa mutane 118 larabawa ne daga kasashe daban-daban, 27 kuma daga kasashen da ba na larabawa ba.
Unguwar Baba Amru ta zama wata babbar tungar 'yan bindiga da suke dauke da makamai suna kaddamar da hare-hare kan jami'anm tsaro da ma fararen hula kamar rahotanni suka tabbatar, amma a cikin kasa da mako guda da ya gabata dakarun gwamnatin Syria sun matsa kaimi wajen ganin sun kawo karshen barazanar 'yan bindiga da suka tare a yankin, tare da hana mutane gudanar da harkokinsu na yau da kullum, lamarin da ya sanya mutane yin magiya ga dakarun kasar da su taimaka musu wajen fitar da 'yan tawayen da suka kafa tunga a yankin suna harbe-harbe.
Yanzu haka dai dakarun gwamnatin Syria sun dawo da doka da oda a yankin Baba Amru da ke birnin Homs, yayin da mutane da suka gudu domin tsira da rayukansu suke ci gaba da komawa gidajensu, amma dakarun gwamnati suna taimaka mutane wajen bin hanyoyin da suka dace domin kauce ma fadawa kan nakiyoyin da 'yan tawaye suka dasa a ko'ina cikin yankin.
Daga karshe ya kara da cewa; bayan da Syria ta samar da sabon kundin tsarin mulki tare da yin sauye-sauye, ko shakka babu daga karshe ita ce za ta yi nasara. 964090