Bangaren kasa da kasa: Sheikh Hasan Alsafar masani da nazarce nazarce dan shi'a a kasar Saudiya ya yi kashedi kan yadda ake yada da cusa tsoro a tsakanin yan shi'a da ahlul baiti da jam'iyu da kungiyoyi ke yi.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: Sheikh Hasan Alsafar masani da nazarce nazarce dan shi'a a kasar Saudiya ya yi kashedi kan yadda ake yada da cusa tsoro a tsakanin yan shi'a da ahlul baiti da jam'iyu da kungiyoyi ke yi.A ranar sha biyu ga watan Isfand na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a cikin hudubar sallar juma'a yayi wannan bayanin cewa: a yau ana yin riko da wata siyasa ta samar da wani yanayi na tsoro da fargaba da halin dar dar a tsakanin mabiya mazhabobin shi'a da ahlul sunna domin ta haka za su cimma mummunan manufofinsu kuma da yardarm Allah ba za su cimma abin da suke son cimmawa ba domin ko ba komi a yau musulmi kansu a hade yake kuma suna fahimtar masu kokarin haddasa rikici a tsakaninsu da kuma ta haka ne suka mulkar da cimma burirrikansu da na wadanda suka turo su a matsayin karnukan farautarsu.
964134