Bangaren al'adu da fasaha: a jiya ne sha uku ga watan Isfand na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a babban dandali na Mir Qum da ke kan hanyar zuwa babbar kasuwa da kuma kusa da Hubbarin Ma'asuma kamar sauran gurare a birnin aka gudanar da tarurrukan juyayi na zagayewar irin wannan rana ta shahadar Ma'asuma ®.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: a jiya ne sha uku ga watan Isfand na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a babban dandali na Mir Qum da ke kan hanyar zuwa babbar kasuwa da kuma kusa da Hubbarin Ma'asuma kamar sauran gurare a birnin aka gudanar da tarurrukan juyayi na zagayewar irin wannan rana ta shahadar Ma'asuma ®.Tun da misalign karfe tara na safiyar ranar sha uku ga watan na Isfand shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya al'ummomi da ya hada mata da maza sun cika da fara taruwa a wannan dandali suna sauraren bayanai da jawabai na malamai daban daban da kawo tarihin rayuwar Ma'asuma da yadda ta rayu da irin zalunci da ta fuskanta daga mahukumatan lokacinta da yadda suka takura mata rayuwa ,Wani bangare na jawaban malaman ya tabo karfin imani da tsoran Allah da ibadodinta da kuma kujewa aikata saboda.
964119