Bangaren al'adu da fasaha, bayan kwashe tsawon shekaru hudu da bude reshen yada labarai na kamfanin dilalncin labaran kur'ani mai tsarki na Iqna a cibiyar bunkasa harkokin ilimi da al'adu da Darul-Hadis, ya zuwa yanzu wannan reshe ya samar da labarai kimanin 3000 a ikin wadannan shekaru.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Darul hadis cewa, tsawon shekaru hudu da bude reshen yada labarai na kamfanin dilalncin labaran kur'ani mai tsarki na Iqna a cibiyar bunkasa harkokin ilimi da al'adu da Darul-Hadis, ya zuwa yanzu wannan reshe ya samar da labarai rubutattu kimanin 700 a ikin wadannan shekaru, sai kuma labarai na hotuna akalla guda 20.
َ A taron da aka gudanar a cibiyar, Ayatollah Rai Shahri ya yi kira ga matasa das u kara himma wajen gudanar da bincike kan harkoki na ilimi, musamman a bangaren kur'ani mai tsarki da hadisi, da kuma kokarin ganin sun fadada irin wadannan ayuka zuwa ga sauran takwarorinsu, ta yadda koyarwar kur'ani za ta zama ta mamaye zukatan matasa musulmi.
Bangaren tace labaran iqna a cibiyar yada ailimi da bunkasa al'adun muslunci ta Darul hadis na saka dukaknin labaransa ne acikin wannan shafi www.iqna.ir/hadis, kuma RuhullahMepour ne ke kula da shirya wadannan labarai a internet.
964291