Bangaren kasa da kasa, abubuwan da suke faruwa a cikin lokutanan nan na cin zarafin musulmi da keta alfarmar abubuwa masu tsarki a cikin addinin muslunci kamar kone kur'ani da aka yi a kasar Afghanistan da sauransu, hakan ya sanya ya zama wajibi musulmi su kara zama cikin fadaka da lura.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa masanin nan damn kasar Afghanistan Ian Mansour ya ce, abubuwan da suke faruwa a cikin lokutanan nan na cin zarafin musulmi da keta alfarmar abubuwa masu tsarki a cikin addinin muslunci kamar kone kur'ani da aka yi a kasar Afghanistan da sauransu, hakan ya sanya ya zama wajibi musulmi su kara zama cikin fadaka da lura kana bin da ake kitsa musu.
Ya ci gaba da cewa a halin yanzu musulmi suna da bukatar su yi fito-na fito da dukkanin makircin da ake kulla musu da kuma addinisu, da nufin rusa shi da zubar da kimarsa a idon duniya, kuma mikewar musulmi da fadakarsu ce kawai za ta ba su damar kawo karshen hakan.
Mansur Tafiq ya ce kur'ani mai tsarki shi ne tsarin mulki da rayuwa acikin addinin muslunci, saboda haka wajibi ne day a rataya kan musulmi su kare wannan littafi da sakon da yake dauke das hi mai tsarki gad an adam, domin kuwa shi ne ya bayar da labarin dukaknin anabawan Allah da suka gabata, kuma ya hada dukaknin sakonnin da suka zo das u daga Allah.
964301