Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na sudaneseonline cewa, za a gudanar da babban taro na mata mabiya addinin muslunci a mataki na kasa da kasa a birnin Tunis fadar mulkin kasar Tunisia tare da halartar masana daga kasashen duniya daban-daban kamar dai yadda kwamitin shirya taron ya sanar.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan taro zai mayar da hankali ne kan muhimamn batutuwa da suka danganci rayuwar mata da kuma irin kalubale da ke gabansu, bisa la'akari da cewa su ne suke da bababn nauyi na kula da tarbiyar iyalia acikin gida, wanda kuma addinin muslunci yan ada ka'idijinsa da dokoki kan yadda ya kamata a tarbiyar da yara da sauransu.
Bisa ga wannan rahoton, jamiyyar nan ta Hizb Al-tahrir mai ra'ayin muslunci a kasar Tunisia, wadda take da magoya baya a ciki da wajen kasar ta sanar cewa babbar manufata ita ce kafa shari'ar muslunci a kasar, wanda kuma da dama daga cikin mutanen kasar Tunisia sun nuna sha'awarsu da musulunci a lokacin zabe, inda suka zabi masu kishin islama.
964429