IQNA

Kamfanin Dillancin Labaran Iqna Na Taka Rawa Wajen Wayar Da Kan Musulmi

20:34 - March 05, 2012
Lambar Labari: 2286190
Bangaren kasa da kasa, a daidai lokacin kafofin yada labarai suka shagaltu da yada karairaki domin kare manufofin ‘yan mulkin mallaka da kawo fitina tsakanin al’ummar musulmi kamfanin dilalncin labaran kur’ani na iqna na kasar Iran yana taka gagarumar rawa wajen wayar da kan musulmi kan wannan makirci da ake kitsa musu.
A wata zantawea da ta hada ta da kamfanin dilalncin labaran iqna, daya daga cikin mambobin kwamitin yaki da manufofin yahudawan sahyuniya a kasar Tunisia Narjis Bin Ubadah ta bayyana cewa, a lokacin kafofin yada labarai suka shagaltu da yada karairaki domin kare manufofin ‘yan mulkin mallaka da kawo fitina tsakanin al’ummar musulmi kamfanin dilalncin labaran kur’ani na iqna na kasar Iran yana taka gagarumar rawa wajen wayar da kan musulmi kan wannan makirci da ake kitsa musu a duniyar kafirci da girman kai da sabon mulkin mallaka.
Ta ci gab ada cewa makiya addinin muslunci ba su gajiyawa wajen shirya makirci wa musulmi, saboda haka ya zama wajibi kan su musulmin da su zama cikin fadaka wajen fahimtar irin wadannan bakaken manufofi, wanda kuma shi ne kokarin da kamfanin dilalncin labaran kur’ani na iqna yake yi dare da rana.
Wannan mata masaniya kan harkokin siyasa da gwagwarmaya da zalunci ‘yan mulkin mallaka ta kara da cewa, abin ban takaici ne yadda kasashen yammacin turai da sauran kasashe makiya muslunci da al’ummar musulmi, suka wayi gari su ne suke juya yunkurin da mutane suke yi na kawo karshen mulkin kama karya, inda ya zama su ne ake yi wa juyin a halin yanzu. 964743
captcha