IQNA

An Kafa Kwamitin Da Zai Kula Da Shirya Gasar Karatun Kur'ani Ta Kasar Qatar

20:55 - March 06, 2012
Lambar Labari: 2286939
Bangaren kasa da kasa, an kafa kwamitin da zai kula da ayyukan shirya gasar karatun kur'ani mai tsarki ta kasa baki daya a kasar Qatar wanda ma'aikatar kula da harkokin addinin muslunci ta kasar take daukar nauyinshiryawa da gudanarwa akowace shekara.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakaltoo daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Al-raya cewa, yanzu haka dai an kafa kwamitin da zai kula da ayyukan shirya gasar karatun kur'ani mai tsarki ta kasa baki daya a kasar Qatar wanda ma'aikatar kula da harkokin addinin muslunci ta kasar take daukar nauyinshiryawa da gudanarwa akowace shekara a kasar, wanda kuma wanna shi ne karo na goma sha tara da za a gudanar da gasar.
Shugaban kwamitin wanda aka dora ma wannan nauyiSayyid Muhammad Mahmud ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu sun fara gudanar da dukaknin ayyukan da suka dace domin shirya wannan gasa, wadda za ta hada dalibai na bangaren kur'ani daga sassan kasar baki daya.
Wanna gasa dai za a kasa ta zuwa kasha bakwai da hakan ya hada da bangarorin harda, gami da kira'a ta tartili da kuma tangim, bugu da kari hakan alkalai za su fitar da dukkanin wadanda suka samu nasara a kowane bangare domin sanar da sunayensu, da kuma bas u kyautar da aka ware domin wannan gasa.
965585


captcha