Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo na palastine Info cewa, kungiyar gwagwarmaya ta Hamas ta yi kakakusar suka da yin Allawadai da sake kame palastinawan da aka saki a kawanakin baya da suke cikin yankunan gabar yammad akogin Jordan domin zalunci irin na yahudawan sahyuniya kan al'ummar palastine.
A cikin bayanin da ta fitar kungiyar ta Hamas ta sheda cewa, wajibi ne dukaknin bangarorin da suka sa hannu wajen gudanar da yarjejeniyar da aka yi da haramtacciyar kasar Isra'ila, das u sanya hannu wajen taka ma yahudawan sahyuniya birki kan wannan tabargaza da suke aikatawa.
A cikin kasa da wata guda, sojojin haramtacciyar kasar sun kame palastinawa sama da dari biyu a cikin garin Alkhalil da ke cikin yankin gabar yamma da kogin Jordan, daga cikinsu kuwa har da wasu palastinawan da suka kwashe tsawon shekaru a cikin gidan kason haramtacciyar kasar Isra'ila.
965290