Bangaren kasa da kasa; hukumar da ke kula da al'adun musulunci da yada ilimi ta Esesko da ke karkashin kungiyar hadin kan kasashen musulmi a wani sako da ta aikewa duniyar musulmi a wannan raneku na tunawa da ranar mata ta duniya ta bukaci kara bawa mata dammar taka rawar gani a lamura da suka shafi zamantakewa da ci gaban al'ummomin musulmi.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: hukumar da ke kula da al'adun musulunci da yada ilimi ta Esesko da ke karkashin kungiyar hadin kan kasashen musulmi a wani sako da ta aikewa duniyar musulmi a wannan raneku na tunawa da ranar mata ta duniya ta bukaci kara bawa mata dammar taka rawar gani a lamura da suka shafi zamantakewa da ci gaban al'ummomin musulmi.Har ila yau a cikin wannan sakon an jinjinawa gwamnatoci da kasashe da kuma hukumomi da kungiyoyi da daidaikun mutane da ke bada dama da taimakawa mata a rawar da suke takawa domin ci gaban al'ummomi daban-daban a kasashen kuma wannan wani nauyi ne na addini mace da namiji su yi aiki tare a tsakanin su a rayuwa ta zamantakewa da sauran bangarori na rayuwa. A gobe ne dai takwas ga watan Maris da ya yi daidai das ha takwas ga wanan Isfand na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya ake raya ranar da aka ware a matsayin ranar mata ta duniya.
966337