IQNA

Shugaban kasar Faransa Zai Kai Ziyara A Babban Masallacin Birnin Paris

20:19 - March 07, 2012
Lambar Labari: 2287697
Bangaren kasa da kasa, shugaban kasar Faransa zai kai ziyara a babban masallacin birnin Paris fadar mulkin kasar a cikin wannan mako kamar yada yadda bangaren hulda da jama’a na ofishin shigaban kasar ta Faransa ya bayar da sanarwa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya naklato daga shafin sadarwa nayanar gizo safir News cewa, Nikola Sarkozy shugaban kasar Faransa zai kai ziyara a babban masallacin birnin Paris fadar mulkin kasar a cikin wannan mako kamar yada yadda bangaren hulda da jama’a na ofishin shigaban kasar ta Faransa ya bayar da sanarwa a jiya.
Bayanin ya ci gab ada cewa daga cikin muhimamn abubuwan da zai yi har da tattaunawa tare da wasu daga cikin jagororin mabiya addinin muslunci an kasar Faransa, da suka hada shugaban m,asallacin Dalil Abubakar dangane da muhimman batutuwa da suka dangaci musulmin kasar Faransa, duk kuwa da cewa gwamnatin Sarkozy ita ce gwamnatin da ta fi nuna matukar adawa da musulmi fiye da dukkanin gwamnatocin da aka yi a kasar.
Wasu dag acikin masu bin diddigin abubuwan da suke kai da komowa suna ganin cewa, wannan ziyarar ba ta rasa nasaba da siyasa, a lokacin da Sarkozy yake ta kara samun bakin jini tsakanin al’ummar kasarsa da kuma sauran kasashen musulmi da na larabawa, yana ta hankorocn ganin ya wanke fuskarsa domin ta yi haske a wurin musulmi.
Daga cikin abubuwan da zai tattaunawa a kansu har da batun musulmin da suka rasa rayukansu wajen kare faransa a lokacin yakin duniya na biyu, wadanda adadinsu ya hauda dubu dari.
966310
captcha