Bangaren kasa da kasa, sama da rabin mutanen kasar Amurka sun yi na’am da uzurin da shugaban kasar Amurka ya nema kan kone kur’ani mai tsarki da sojojin kasarsa suka yi a kasar Afghanistan, tare da bayyana hakan da cewa shi ne ya dace domin kuwa an tafka babbar tabargaza.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo na DAWN cewa, sama da rabin mutanen kasar Amurka sun yi na’am da uzurin da shugaban kasar Amurka ya nema kan kone kur’ani mai tsarki da sojojin kasarsa suka yi a kasar Afghanistan, tare da bayyana hakan da cewa shi ne ya dace domin kuwa an tafka babbar tabargaza, kuma hakan zai kara kyamar Amurka atsaknainta da kasashen msuulmi da na larabawa.
Bayanin ya ci gaba da cewa, wannan mataki yana nuni da cewa ana samun gagarumin canji a cikin tunanin mutanen kasar Amurka, inda hakan ke nuni da cewa ba su amince da siyasar kasar ta yin batunci ga addinin muslunci ba, da kuma yadda kashi sittin da shida cikin dai na mutanen kasar suka nuna amincewa da neman uzuri dag amusulmi, saboda kone kur’ani da sojojin Amurka suka yi.
Kimani rabin mutanen kasar Amurka sun yi na’am da uzurin da shugaban kasar Amurka ya nema kan kone kur’ani mai tsarki da sojojin kasarsa suka yi a kasar Afghanistan, tare da bayyana hakan da cewa shi ne ya dace domin kuwa an aikata abin da ba daidai ba.
966612