Bangaren kasa da kasa:Muhammad Musawi shugaban komitin musulmin faransa ya bayyana cewa; ba za taba amincewa da yarda yan takarar neman shugabanncin kasar Faransa su yi amfani da musulmi ko lamarin musulmi da zama ragon layyarsu na cin burinsu na siyasa.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: Muhammad Musawi shugaban komitin musulmin faransa ya bayyana cewa; ba za taba amincewa da yarda yan takarar neman shugabanncin kasar Faransa su yi amfani da musulmi ko lamarin musulmi da zama ragon layyarsu na cin burinsu na siyasa. Shugaban komitin musulmin na kasar Faransa yana mamakin yadda wasu yan takarar neman shugabancin kasar ta Faransa ke wasa da hankalin jama'ar kasar da kuma kokarin yin amfani da addini domin cimma manufarsu ta siya.a cikin wani jawabi ne da firaministan faransa karkashin mulkin Nikolas Sarkozi ya yi wata Magana ta izgili da neman jan hankalin al'ummar Faransa na cewa yadda musulmi ke yanka dabbobi ya sabawa irin na zamani da hakan yake son yin suka kan addinin musulunci da musulmi da ta wannan zai sa wasu su jefa masa kuri'a kamar yadda suka saba a kullum idan zabe ya zo sais u yi wata Magana ta suka da daukan matakai na takurawa musulmi a kasar ta Faransa.
967092