IQNA

Kasashen Afirka Sun Rungumi Tsarin Tattalin Arziki Na Musulunci

Bangaren siyasa da zamantakewa; binciken da mu'assisar Baitka li'abhas ya yi nuni da cewa; rikicin tattalin arziki da duniya ke fuskanta a yau ya sa kasashen Afirka sun rungumi tsarin tattalin arziki irin na musulunci.


Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: binciken da mu'assisar Baitka li'abhas ya yi nuni da cewa; rikicin tattalin arziki da duniya ke fuskanta a yau ya sa kasashen Afirka sun rungumi tsarin tattalin arziki irin na musulunci. A cikin wannan rahoto an bayyana cewa kasashen arewacin Afirka da kuma kasashe irin su Keniya,Mali Senegal da Afrika ta kudu sun maida hankali a yan shekarun nan wajan yin hulda ta kasuwanci da tsarin tattalin arziki day a yi daidai da tsari irin na addinin musulunci.A wani bangare na rahoton ya bayyana cewa; a nahiyar afrika akwai cibiyoyi sama da talatin da takwas na masu ma'amalar kudi da tattalin arziki irin ta muusulunci da k eke jibge a cikin nahiyar kuma da dama daga cikin kasashen Afrika sun bawa bankunansu dammar yin gyara da kawo canji a cikin dokokin dokokin bankokinsu dam aye gurbinsu da na tsarin musulunci. Kuma abin tuni a nan wannan sakamakon bincike a ranar sha uku ga watan Isfand na shekara ta dubu daya da darii uku da tis'in hijira shamsiyasa aka watsa shi.

967321