IQNA

An Gudanar Da Tarukan Cika Shekaru 170 Da Shigar Addinin Muslunci Uganda

17:57 - March 08, 2012
Lambar Labari: 2287983
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da tarukan cika shekaru 170 da zuwan addinin muslunci kasar Uganda a birnin Kampala fadar mulkin kasar, wanda ya samu halartar dubban mutane da suka hada da jami'an gwamnati da kuma shugabannin cibiyoyin addini.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na On Islam cewa, a jiya ne aka gudanar da tarukan cika shekaru dari da saba'in da shigar muslunci kasar Uganda a birnin Kampala , tare da halartar dubban mutane da suka hada da jami'an gwamnati da kuma shugabannin cibiyoyin addini na musulunci da ma kiristoci, kuma anan aka karanta bayanin shugaba Mrsivini na kasar kan muhimmancin hadin kai da zaman lafiya tsakanin mabiya dukkanin addinai, tare da taya musulmi murnar wannan rana.
A cikin bayanin day a rubuta wanda wakilinsa ya karanta a gaban mahalarta taron, shugaban kasar ta Uganda ya jinjinawa al'ummar musulmi kan irin gagarumar gudumawar da suke bayarwa a fannoni da dama a kasar, da hakan ya hada da shiga cikin dukkanin harkokin bunkasa ci gabanta da tattalin arzikinta.
A jawabinsa dangane da bikin cikan shekaru 170 da shigar addinin Musulunci kasar Uganda; shugaban kasar Yoweri Museveni ya taya al'ummar musulmin Uganda murnar cikin shekaru 170 da shigar addinin Musulunci cikin kasar Uganda tare da jinjina musu kan irin gagarumar gudumawar da suke bayarwa a fannoni da dama na kasar musamman a bangaren bunkasa harkar tattalin arziki, siyasa da zamantakewar al'umma.
Museveni ya bayyana cewar addinin Musulunci ya shiga cikin kasar Uganda ne ta hanyar Larabawa 'yan kasuwa da suke gudanar da harkar kasuwanci a nahiyar gabashin Afrika, sannan addinin na Musulunci ya ci gaba da yaduwa da taimakon malamai da suke gudanar da wa'azi da fadakar da al'umma koyarwan addinin Musulunci.
A halin yanzu haka dai yawan musulmi a kasar sun kai kashi 14 cikin dari a tsakanin al'ummar kasar Uganda da adadinsu ya kai miliyan 32.
967196

captcha