Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-taufiq cewa, al'ummar kasar Bahrain sun tabbatar wa duniya da cewa su ne masu neman sauyi ta hanyar demokradiyya ta hakika kamar yadda hakan ya tabbata daga jerin gwanon da suka gudanar a wannan juma'a da ta gabata inda suka yi zanga-zanga mafi girma tun bayan da aka fara boren neman sauyi.
Bayanin ya ci gaba da cewa, dubban dubatan mutanen kasar Bahrain ne suka amsa kiran Shugaban Majalisar Malaman addinin kasar Ayatullahi Sheikh Isa Kasim na fita zanga zangar nunawa sarakunan kasar cewa masu adawa da tsarin sarautar kasar ba tsiraru ne kamar yadda Sarki Hamad Bin Isa ya kirasu a kwanakin bayan ba.
Gidan television na Al-Alam da ke watsa shirye shiryensa da harshen larabci a nan Tehran ya nuna dubban mutanen kasar wadanda suka cika titunan garuruwan Diraz da kuma Sa'ar a gabacin kasar suna rera taken "Labbaika Ya Bahrain" suna kuma kira ga kawo karshen tsarin zalunci da danniya wanda yan gidan Aali Khalifa suke kansa fiye da shekaru 200 da suka gabata.
Jam'iyyar Al-Wafeq, jam'iyyar yan adawa mafi girma a kasar ta bayyana cewa "lokaci yayi wanda za'a tabbatar da bukatun mafi rinjayen mutanen kasar Bahrain." Hakama sauran jam'iyyun adawar kasar sun bukaci kawo a karshen mamayen da jami'an tsaron kasar saudia sukewa kasar da kuma dakatar da tallafin da kasashen waje suke bawa Sarakunan kasar don murkushe yan adawa.
Wasu kafafen yada labarai sun kiyasta yawan mutanen da suka amsa kiran babban malamin, sun fi rabin jimmillan mutanen kasar gaba daya. Ayatullahi Sheikh Isa Kasim da sauran manya manyan malaman addini da yansiyasar kasar Bahrain da dama suna sahun gaba a cikin wannan fitowar na tabbatarwa duniya cewa sarakunan kasar Bahrain wadanda suke murkushe borin mutanen kasar da karfin makami tun fiye da shekara guda su ne tsiraru ba masu adawa da gwamnatin kasar ba. 968324