Bangaren kasa da kasa: taron karawa juna sani kan sadaukar da kai da riko da gwagwarmaya da aka gudanar a ranar larabar da ta gabata sha bakwai ga watan Isfand na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamiya a birnin Karbala na kasar iraki.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; taron karawa juna sani kan sadaukar da kai da riko da gwagwarmaya da aka gudanar a ranar larabar da ta gabata sha bakwai ga watan Isfand na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamiya a birnin Karbala na kasar iraki.An jiyo daga gidan talbijin na Al'alam da ke watsa shirye-shiryensa ta hanyar tauraron dan adam cewa a gudanar da wani taron karawa juna asani kan muhimmancin yin riko da tafarkin gwagwarmaya a garin Karbala na kasar Iraki inda aka jinjina muhimmancin yin riko da hanyar gwagwarmaya domin fuskantar duk wani mataki na mulkin mallaka da shiga sharo ba shanun Amerika da katsalandarta a cikin harkokin kasashen cikin gida . Har ila yau mahalarta wannan taron sun bayyana cewa: daya dayan dalilin ficewar sojojin Amerika daga iraki ba tare da Amerika ta shirya ficewar bas hi ne gwagwarmaya da tsayin dakan da al'umma da gwamnatin Iraki da kungiyoyin kasar suka nuna.
968233