Bangaren kasa da kasa;a lokacin da matashi dan kasar Tunusiya ya cinnawa kansa wuta da kansa bai yi zaton wannan wuta zata rikide ta zama wani sauyi da canji a tsakanin kasashen larabawa day a hada yankin gabas ta tsakiya da arewacin Afirkka amma a yau yadda ake tafiyar da lamarin a wani sabon salo a yankin gabas yana son ya canja fadakarwar musulmi a yankin.
Kamfanin dillancin labarai na iKna da ke kula da harkokin kur'ani mai tsarki a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: a lokacin da matashi dan kasar Tunusiya ya cinnawa kansa wuta da kansa bai yi zaton wannan wuta zata rikide ta zama wani sauyi da canji a tsakanin kasashen larabawa day a hada yankin gabas ta tsakiya da arewacin Afirkka amma a yau yadda ake tafiyar da lamarin a wani sabon salo a yankin gabas yana son ya canja fadakarwar musulmi a yankin.Kanal Kadafi ya kamu da cutar giyar mulki da jiji da kai na girman kai da dagwawa ko a mafarki bai yi zaton al'ummar kasarsa za suma amince da fitowa kan tituna domin kalubalanci mulkinsa da neman ya sabka daga kan karagar mulkin wannan kasa day a yi sheka da shekaru yana tafiyar da mulkinta yadda ya ga dama amma sai gashi an wani gari an kifar da gwamnatinsa da ma kasha shi lamarin da zama tamkar a mafarki to amma babu wanda ya cancanji daukan darasi kamar su sabbin mahukumtan Libiya da suka samu wannan garabasa suna zaune suma a daidai lokacin dab a su zato bas u tsammahani .Wani abu mai muhimmanci day a kama ta su sani shi ne matukar bas u yi ahankali da gudanar da mulkin adalci a wannan kasa kawo zai iya juyewa da mujiya kamar yadda abin day a faru da Kaddafi mai jiji da kai da karfin mulki ya tabbatar da abin da yan iya Magana ke cewa dan hakin da ka rena shi ke tsone maka ido.
969779