Bangaren kasa da kasa: masu yin riko da addinin musulunci a Bahrain sun fitar da bayanin cewa: ranar sha uku ga watan Maris wadda ta yi daidai da ashirin da uku ga watan Isfand na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya wato jiya ke nan an sanya mata suna ranar kasa ta gwagwarmya da fuskantar yan mamaye na Saudiya a fadin kasar Bahrain.
Kamfanin dillancin labarai na iKna da ke kula da harkokin kur'ani mai tsarki a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: masu yin riko da addinin musulunci a Bahrain sun fitar da bayanin cewa: ranar sha uku ga watan Maris wadda ta yi daidai da ashirin da uku ga watan Isfand na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya wato jiya ke nan an sanya mata suna ranar kasa ta gwagwarmya da fuskantar yan mamaye na Saudiya a fadin kasar Bahrain.Majiyar labarai ta Fajrbh cewa a ranar ashirin ga watan Isfand na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya wannan kungiyar ta fitar da wannan sanarwa da a ciki take kiran al'ummar wannan kasa da su raya wannan rana ta gwagwarmaya da fada da mamayen sojojin Saudiya a wannan kasa da suke danne al'ummar kasar Bahrain masu son a kawo canji da sauye sauye a siyasar kasar ta Bahrain da kawo karshen danniya da zaluntar yan kasar da masarautar Bahrain da gwamnatin Bahrain ke yi amma masarautar da kuma goyan bayan mahukumtan Saudiya da kuma wasu kasashen yammacin Turai musamman Amerika sun tashi haikan da amfani da sojojin da manyan makamai da nuna karfi day a wuce kima wajan murkushe masu gudanar da wannan zanga zanga a Bahrain amma ba tare da sun cimma mummunar manufarsu ba.
969803