Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Palestine Info cewa, kungiyar hadin kan likitoci an kasashen larabawa ta bukaci kai taimakon gaggawa ga al'ummar yankin Zirin Gaza da suke fuskantar mummnan ta'addanci da keta alfarmar dan adam daga haramtacciyar kasar Isra'ila bayan da gwamnatocin musulmi da na larabawa suka nuna ko inkula.
Fira ministan gwamnatin haramtaciyar kasar Isra'ila ya jaddada aniyarsa na ci gaba da kaddamar da hare haren wuce gona da iri kan yankin Zirin Gaza da ke Palasdinu.
Fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila Benyamin Natenyahu a jiya lahadi ya jadadda cewa: Sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila zasu ci gaba da kai hare hare kan yankin Zirin Gaza har sai sun kai ga murkushe 'yan gwagwarmayar Palasdinawa.
A nashi bangaren fira ministan Palasdinawa a yankin Zirin na Gaza Isma'il Haniyya ya yi Allah wadai da hare haren ta'addancin da sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila ke kai wa kan yankin, tare da bayyana cewar sojojin suna kai hare haren ne kan fararen hula da sunan kashe 'yan gwagwarmaya.
A cikin kwanaki uku da sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila suka kwashe suna kai hare haren ta'addanci kan yankin Zirin Gaza, akalla mutane 18 ne suka yi shahada wasu da dama kuma suka jikkata.
969372