Bangaren kasa da kasa: an fara gina masalllaci mafi girma a nahiyar turai tare da hadin guiwar daya daga cikin kamfani mafi girma na turkiya ya dauki dawainiyar ginawa a birnin Kolon na kasar Jamus.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai tsarki a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: an fara gina masalllaci mafi girma a nahiyar turai tare da hadin guiwar daya daga cikin kamfani mafi girma na turkiya ya dauki dawainiyar ginawa a birnin Kolon na kasar Jamus. An nakalto daga jaridar al'yaum sab'a da ake bugata a kasar Masar cewa: daya daga cikin kamfanin mafi girma a kasar Turkiya ta dauki nauyin fara gina masallaci mafi girma a birnin Kolon na kasar Jamus .wannan masallaci za a gina shi kan kudi tsaba miliyon talatin da hudu na Yuro kuma zai dauki masallata a dubu biyu a lokaci guda kuma wanna zai bawa musulmi a nahiyar turai musamman da ke zaune a wannan birnin dammar gudanar da harkokin addininsu da sallo da ibadodinsu. Daga karshe an bayyana cewa a shekara mai zuwa ce za a kammala gina wannan masallaci ma'ana za a kwashe tsawon shekara daya ne ana gina wannan masallacin.
969999