Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, Kofi Annan tsohon sakatare janar na majalisar dinkin duniya ya kammala tattaunawar da ya gudanar a kasar Syria tare da dukaknin bangarorin rikicin kasar tare da sa ran za ashawo matsalar da ake fama da ita a kasar wanda kasashen yammacin turai da karnukan farautarsu daga cikin kasashen larabawa suka kirkiro.
Gwamnatin kasar Syria ta sanar cewa 'yan ta'adda da suke dauke da makamai a kasar ne suke da alhakin kasha fararen hula da kuma tozarta gawawwakinsu, tare da daukar hotunansu domin domin sakawa a kafafen yada labarai na kasashen da ke gaba da Syria.
Ministan watsa labaran kasar Syria Adnan Mahmud ne ya bayyana hakan a yau a lokacin da yake zantawa da wasu kafofin yad alabarai, inda ya ce 'yan ta'adda da suke dauke da makamai a kasar Syria ba su banbanta tsakanin jami'in tsaro ko farar hula, domin kuwa suna kallon duk wanda bai shiga cikinsu ba a matsayin makiyi kuma jininsa ya halasta, a kan haka ne suke kashe fararen hula, kuma su dauki hotunan gawawwakinsu domin su aika ga wasu kafofin yada labarai da suke yi musu farfaganda, ta yadda za a zargi sojojin gwamnati da aikata hakan.
A wata zantawa da ta hada wasu daga cikin iyalan wadanda aka nuna gawwakinsu da manema labarai sun bayyana cewa, 'yan bindiga ne suka kashe dangin nasu, yayin da wasu suka sheda cewa 'yan ta'addan sun sace dangin nasu ne tun kimanin wata guda da ya gabata, kuma sai suka ga hotunan gawawwakinsu a wasu kafofin yada labarai ana dora alhakin mutuwarsu kan sojojin gwamnatin kasar, inda suka kore wannan labara tare da dora alhakin mutuwar danginsu a kan 'yan bindiga.
970519