Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-risalah cewa, pira ministan Hamas a yankin zirin Gaza Isma’ila Hnaiyya, ya bayyana cewa al’ummar palastinu ba za ta taba mika wuya manufofin haramtavcciyar kasar isra’ila ba duk kuwa da irin ta;’addancin da take yi kan fararen hula musamman a yankin zirin gaza ba tare da kasashen amsu raya kare hakkin bil adama sun uffan kan hakan ba maimakon yin Allawadai ma sai kara kusantar ta da wasu kasashen larabawa suke yi.
Jamhuriyar muslunci ta Iran ta yi Allawadai da kisan gillar da haramtacciyar kasar Isra'ila take yi kan al'ummar palastine da ke yankunan zirin gaza, a cikin wani bayani da ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran ta fitar yau, ta kirayi gwamnatocin kasashen musulmi da sauran kasashe masu sauran lamiri a duniya da su safke nauyin da ya rataya kansu na kare al'ummar palastinu da sojojin yahudawa ke ci gaba da yiwa kisan gilla kwanaki uku a jere, tare da bayyana cewa wannan aiki na dabbanci yana faruwa ne sakamakon nuna halin ko in kula da musulmi suke yi kan dukkanin ta'asar da haramtacciyar kasar Isra'ila take tafkawa kan al'ummar palastinu.
Bayanin ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Iran ya kara cewa, ina gwamnatocin da ke da'awar kare hakkokin fararen hula a wasu kasashe, me yasa ba a ji duriyarsu kan kisan kiyashin da sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila suke yi wa al'ummar palastinu ba, rahotanni daga yankin zirin Gaza sun tabbatar da cewa adadin mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren na sojojin yahudawa daga ranar Juma'ar da ta gabata zuwa zuwa yau, ya kai muane 23, da suka hada da kananan yara da mata.
970336