IQNA

Beljik Ta Yi Allah Wadai Da Harin Da Aka Kai Wa Cibiyar Musulunci Ta Yan Shi'a A Buksel

12:14 - March 14, 2012
Lambar Labari: 2291729
Bangaren kasa da kasa: Jawanl Mika'il ministan cikin gida na kasar Beljuim ya yi Allah wadai da harin da aka kai da kona masallacin kuma gurin ibada na imam Rida nay an Shi'a a birnin Buksel na kasar.


Kamfanin dillancin labarai na iKna da ke kula da harkokin kur'ani mai tsarki a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: Jawanl Mika'il ministan cikin gida na kasar Beljuim ya yi Allah wadai da harin da aka kai da kona masallacin kuma gurin ibada na imam Rida nay an Shi'a a birnin Buksel na kasar.An nakalto daga majiyar labarai ta levif cewa a ranar ashirin da biyu ga watan Isfand na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya aka kai wa masallacin Imam Rida (AS) da cinna masa wuta da kona wannan guri na ibada na mabiya mazhabar shi'a a birnin Buksel na kasar Beljuim inda ministan cikin gida na wannan kasar bayan yin Allah wadai ya fito fili karara ya bayyana cewa: babu wani dalili da za a iya gabatarwa da zai wanke wannan mummunan aiki. Ya kara da cewa:wanda ya aikata wannan mummunan aiki ya yi sanadiyar rasa rayukan mutane biyu musulmi yan kasa kuma wannan wani aiki ne na makircin haddasa rikici a tsakanin mazhabobin musulmi a wannan kasa da yada wannan fitina a fadin kasashen Turai.

971296
captcha