Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Almanar cewa, an kame matashin da ya keta alfarmar kur'ani mai tsarki a kasar Tunisia a yankin mahdiyya kuma yanzu haka lamarinsa na gaban kuliya domin fuskantar hukunci kan wannan danyen aiki da ya tafka, kuma za a ci gab ada bincike a kan lamarin koda wasu suna da hannu wajen yin amfani da hakan domin kawo rikici da tashin hankali a kasar.
A wani labarin kuma na daban, majalisar soji mai mulki a kasar Masar ta yi barazanar ruguza majalisar kasar matukar dai 'yan majalisar suka kada kuri'ar rashin amincewa da gwamnatin firayi ministan kasarKamal Janzuri.
Rikici dai na ci gaba da bayyana tsakanin sabbin 'yan majalisar da gwamnatin firayi ministan Al-Janzurin ne wanda 'yan majalisar suke ganinta a matsayin ci gaban tsohuwar gwamnatin tsohon shugaban kasar da aka fatattaka Hosni Mubarak lamarin da ya sanya 'yan majalisar fara tunanin kada kuri'ar rashin amincewa da gwamnatin lamarin da zai kawo karshenta.
'Yan majalisar dai sun jima suna nuna rashin jin dadinsu da yadda gwamnatin kasar Masar din take gudanar da ayyukanta wadanda suka ce ba su dace da ayyukan wata gwamnati wacce aka kafa ta bayan wani juyin juya hali ba.
A bisa kundin mulkin kasar Masar din da a sojojin suka tabbatar da shi, majalisar sojin wacce ita ma take ci gaba da fuskantar suka tana da hakkin rusa majalisar kasar.
970845