IQNA

Wasu Masu tsatsuran Ra'ayi Sun kai Hari Kan wani Masallaci A Brussel

19:08 - March 14, 2012
Lambar Labari: 2291995
Bangaren kasa da kasa, majalisar musulmin kasar Belgium ta sanar cewa masu akidar salafiyanci da kafirta sauran musulmi ne suka kaddamar da hari kan masallacin Imam Rida (AS) da ke birnin Brussel inda suka kone shi kurmus.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tf1 cewa, majalisar musulmin kasar Belgium ta sanar cewa masu akidar salafiyanci da kafirta sauran musulmi ne suka kaddamar da hari kan masallacin Imam Rida (AS) da ke birnin Brussel inda suka kone shi kurmus tare da yin kisan gilla kan limamin masallacin, bayan bude masa wuta a lokacin da yake sallar asubahi.
Wannan rahoto da majlasar malaman addinin muslunci na kasar ta Belgium ya yi nuni da cewa, yanzu haka an shiga gudanar da bincike kan wannan lamari, kuma ba za a bar irin wannan lamari ya tafi hakan nan ba tare da an hukunta wadanda suke da hannu kai tsaye a cikin wannan babbar ta'asa.
Babbar majalisar musulmin kasar Belgium ta sanar cewa masu akidar salafiyanci da kafirta sauran musulmi wadanda suka kaddamar da hari kan masallacin Imam Rida (AS) da ke birnin Brussel, su ne bababr barazana ga musulmin kasar da ma sauran musulmi na duniya, domin kuwa akidarsu tana rusa addini ne da kyakyawan manufofinsa da koyarwarsa.
971046

captcha