IQNA

Majalisar Dokokin Masar Ta Bukaci Da Kori Jakadan Isra'ila Daga Kasar

19:08 - March 14, 2012
Lambar Labari: 2291996
Bangaren kasa da kasa, 'yan majlaisar dokokin kasar sun mayar da martini mai zafi kan kisan gillar da haramtacciyar kasar Isra'ila take yi kan al'ummar palastinu mazauna yankin zirin Gaza a cikin wannan mako, inda suka bukaci da a kori jakadan na Isra'ila da ke cikin birnin Alkahira.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo almisrialyaum cewa, 'yan majlaisar dokokin kasar sun mayar da martini mai zafi kan kisan gillar da haramtacciyar kasar Isra'ila take yi kan al'ummar palastinu mazauna yankin zirin Gaza a cikin wannan mako, inda suka bukaci da a kori jakadan na Isra'ila da ke cikin birnin Alkahira batare da wani bata lokaci ba.
Majalisar soji mai mulki a kasar Masar ta yi barazanar ruguza majalisar kasar matukar dai 'yan majalisar suka kada kuri'ar rashin amincewa da gwamnatin firayi ministan kasarKamal Janzuri, rikici dai na ci gaba da bayyana tsakanin sabbin 'yan majalisar da gwamnatin firayi ministan Al-Janzurin ne wanda 'yan majalisar suke ganinta a matsayin ci gaban tsohuwar gwamnatin tsohon shugaban kasar da aka fatattaka Hosni Mubarak lamarin da ya sanya 'yan majalisar fara tunanin kada kuri'ar rashin amincewa da gwamnatin lamarin da zai kawo karshenta kwata-kwata.

Wadannan 'yan majalisar dai sun jima suna nuna rashin jin dadinsu da yadda gwamnatin kasar Masar din take gudanar da ayyukanta wadanda suka ce ba su dace da ayyukan wata gwamnati wacce aka kafa ta bayan wani juyin juya hali ba a bisa kundin mulkin kasar Masar din da a sojojin suka tabbatar da shi, majalisar sojin wacce ita ma take ci gaba da fuskantar suka tana da hakkin rusa majalisar kasar ta Masar.

971128
captcha