Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a zantawar da ta hada shi da masani kan harkokin siyasar kasashen larabawa Abdulazim Almagaribi ya bayyana cewa, irin yadda masu kishin islama suka kai ga madafun iko a wasu kasashe na larabawa da su kai fama da rikici har ya kia ga kawo karshen shugabanninsu hakan ya mayar da hannun agogo baya a jankoron haramtacciyar kasar Isra’ila kan al’ummomin yankin, musamman a gabas ta tsakiya da arewacin Afirka.
Ya ci gaba da cewa tun daga lokacin da aka fara bore a kasar Tunisia wanda shi ne bore na farko da aka yi a kasashen larabawa da kai ga ballewar sauran tashe-tashen hankula a yankin baki daya, daga lokacin hantar haramtacciyar kasar Isra’ila ta kada, domin kuwa ta sani sarai cewa, hakan ba zai zama maslaha gare ta a nan gaba ba.
Masanin ya ce ya imanin cewa irin yadda masu kishin islama suka kai ga madafun iko a wasu kasashe na larabawa da su kai fama da rikici har ya kia ga kawo karshen shugabanninsu hakan ya mayar da hannun agogo baya a jankoron haramtacciyar kasar yahudawa ga kasashen larabawa da na musulmi.
Duk da cewa makiya suna yin mafani da wasu karnukan farautarsu daga cikin shugabanni da sarakunan larabawa domin su m,ayar da boren na larabawa yadda zai amfanar da gwamnatin yahudawan da kasashen turai.
971979