Bangaren kasa da kasa: musulmi a birnin Burksel na kasar beljuim a ranar ashirin da takws ga watan Isfand na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya sun gudanar da wata gagaramar zanga zangar adawarsu da kona masallacin Imam Rida (AS) nay an shi'a da wani wahabiye mai tsotsoran ra'ayin addini ya yi.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna ne da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ya watsa rahoton cewa: musulmi a birnin Burksel na kasar beljuim a ranar ashirin da takws ga watan Isfand na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya sun gudanar da wata gagaramar zanga zangar adawarsu da kona masallacin Imam Rida (AS) nay an shi'a da wani wahabiye mai tsotsoran ra'ayin addini ya yi. An nakalto daga majiyar labarai ta safir News cewa shugabannin masallacin kuma cibiyar harkokin addini ta Imam Rida a birnin na Bruksel sun bukaci duk wani musulmi mazaunin babban birnin an Beljuim shi 'a ne ko ahlul sunna da ya halarci wannan gagaramar zanga zangar yin Allah wadai da wannan danyan aiki na wani wahabiya yayi na cinnawa masallacin wuta da yayi sanadiyar shahadar limamin masallacin . Musulmi a sauran kasashen duniya ma na ci gaba da yin Allah wadai da wannan mummunan aiki tare da tofa albarkacin bakin sun a yin Allah wadai da irin wannan aiki .
972840