Bangaren kasa da kasa;a ranar ashirin da hudu ga watan Isfand ne na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a wani babban masallacin birnin Paris fadar mulkin kasar Faransa aka kaddamar da wata cibiya ta girmamawa da kuma tunawa da sojoji musulmi da suka rasa rayukansu wajan kare kasar ta Faransa.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna ne da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ya watsa rahoton cewa: a ranar ashirin da hudu ga watan Isfand ne na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a wani babban masallacin birnin Paris fadar mulkin kasar Faransa aka kaddamar da wata cibiya ta girmamawa da kuma tunawa da sojoji musulmi da suka rasa rayukansu wajan kare kasar ta Faransa.An nakalto daga majiyar labarai ta yabiladi cewa:" a wajan wannan buki na kaddamar da wannan cibiya ta tunawa da sojojin faransa kuma musulmi da suka sadaukar da rayuwarsu wajan kare kasar ta Faransa a lokacin yakin duniya na biyu an samu halartar shugaban kasar faransa Nicola Sarkozi da Klod Guian ministan cikin gina na kasar Faransa da Gerad Lunce ministan tsaron kasar Faransa da kuma Dalil Bubakar shugaban wannan cibiya da kuma babban masallacin birnin Faransa da kuma Muhammad Musawi shugaban komitin musulmin kasar Faransa.Duka wadanda suka halarci wannan guri sun nuna gamsuwa da jin dadinsu kan wannan tunani na kaddamar da wannan cibiya da kuma yadda wadannan musulmi suka sadaukar da rayuwarsu wajan kare kasar Faransa a lokacin yakin duniya na farko.
972853