IQNA

Wata Kotu A Faransa Kakaba Mutane Hudu A Gidan yari Saboda Sun Haramta Kayan Isra'ila

12:54 - March 17, 2012
Lambar Labari: 2292934
Bangaren kasa da kasa: wata kotu na garin Bobigny na kasar Faransa ta yankewa wasumutane hudu masu goyan bayan al'ummar Palasdinu da kae zalunta zama a gidan yari saboda sun haramta kayayyakin da gwamnatin Haramtacciyar kasar Isra'ila ke kerawa kuma bayan daure su a gidan yarin kuma an ci su tarar kudade.



Kamfanin dillancin labarai na Ikna ne da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ya watsa rahoton cewa: wata kotu na garin Bobigny na kasar Faransa ta yankewa wasumutane hudu masu goyan bayan al'ummar Palasdinu da kae zalunta zama a gidan yari saboda sun haramta kayayyakin da gwamnatin Haramtacciyar kasar Isra'ila ke kerawa kuma bayan daure su a gidan yarin kuma an ci su tarar kudade.An nakalto daga majiyar labarai ta maville cewa; wata kotun kama karya a birnin Bobigny na kasar faransa ta yankewa wasu mutane hudu zama a gidan yari na tsawon watanni hudu kowannansu tare da cin su tara kudi daga yuro dubu daya zuwa dubu biyu kuma leifinsu sun kiran mutanan garin das u kauracewa kayan da ke fitowa da kuma gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ke kerawa kuma an zarge su ne da laifin nuna wariya da ha'inci . wadannan mutane da aka yankewa wannan hukumci na zalunci su ne Maha Barbet da Ulariish Barbat da Ayat Ali da kuma cikin na hudunsu shi ne Jakalin Zamur mambobi a kungiyar Yoron Palsdinu kuma ana zarginsu da leifinda suka aikara a sheakara ta dubu biyu da tara miladiya kuma sai a ranar ashirin da biyar ga watan Isfand na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya aka yanke masu wannan hukumci.Tuni kungiyoyi da hukumomi n akare hakokin bil adam a ciki da wajan faransa suka bukaci a sako su da cewa wannan hukumci ne na siyasa da nuna wariya kan musulmi da addininsu.
972891
captcha