Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: mai kula da ofishin firaministan kasar Malaishiya a ranar ashirin da hudu ga watan Isfand na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya ya bada labarin mataki da matsayar gwamnatinsa ta taimakawa kungiyoyi da cibiyoyi na musulmi da goyan bayansu.Nasir Bin AbdulAziz Muhammad mai kula da ofishin firaministan kasar ta Malaishiya ne a lokacin bukun bude wata cibiya ta tuni da ma'aikin Allah tsira da amincin allah ya tabbata a gare shi da kuma alayan gidansa tsarkaka ya bayyana cewa: wannan kasance tasa a tsakanin yan uwansa musulmi na isar da sako da bayyana cewa; gwamnatin kasar a shirye take ta taimakawa musulmi da kungiyoyi da cibiyoyi na musulmi a wannan kasa.Har ila yau ya bada albishir da labarin cewa: akwai wani adadi na kudadai da gwamnatinsu ta ware domin kara fadada dangantakarta da kungiyoyi da cibiyoyi na musulmi da kuma a tsakaninta da daidaikun musulmin a kasar. Kuma za su kara fadada dangantakar kasuwanci a tsakanin gwamnatinsa da sauran cibiyoyi na musulmi day ace wannan bangare ma wani abu ne mai muhimmanci da za a inganta da yin la'akari das hi.
973401