IQNA

A Pakistan Taro Kan Fadakar Da Al'ummar Musulmi

15:35 - March 18, 2012
Lambar Labari: 2293585
Bangaren nazari da ilimi: a ranar ashirin ga watan farvardin na shekara mai kamawa wato watan farko na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in da daya hijira shamsiya za a gudanar da wani taro a garin Jahang na lardin Panjab na kasar Pakistankan fadakar da al'ummar musulmi da majalisar hadin kan al'ummar Pakistan ta garin ta dauki dawainiyar gudanarwa.



Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: a ranar ashirin ga watan farvardin na shekara mai kamawa wato watan farko na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in da daya hijira shamsiya za a gudanar da wani taro a garin Jahang na lardin Panjab na kasar Pakistankan fadakar da al'ummar musulmi da majalisar hadin kan al'ummar Pakistan ta garin ta dauki dawainiyar gudanarwa.Majalisar hadin kan musulmi da kuma al'ummomin wannan kasa ta bayyana cewa ta shirya wannan taro ne a ranar ashirin ga watan farvardin na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in da daya zai hada da tattaro manyan yan siyasa malaman addini ,da malaman adabi da yan siyasa da kuma masu kula da harkokin al'adu da kuma uwa uba dubban musulmi da za su halarci wannan taro. Har ila yau manyan malamai na shi'a da sunna za su gabatar da jawabai a gurin wannan taro da za su tabo muhimmancin hadin kai da fadakarwar al'ummar musulmi musamman a wannan lokaci da babban kalubalan da ke a gabansu tun kafin lokaci ya kure masu.

972308
captcha